Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta damu matuka kan halin matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar musamman ma na hauhawar farashin kayayyaki.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin karbar wani daftari na sake duba ayyukan ma’aikatun gwamnati da aka kafa bayan gabatar da rahoton kwamitin Oronsaye kan sake fasalta hukumomin gwamnatin tarayya tsakanin watan Oktoban 2012 zuwa Oktoban 2022.
Gwamnatin Naeriya ta ce ta damu game da halin tsadar rayuwa da ‘yan kasar ke ciki, inda ta ce tana yin duk abin da ya kamata domin saukaka abubuwa.
Boss Mustapha ya ce mambobin da aka bai wa aikin sake fasalta ma’aikatun gwamnatin na da hazaka da kuma kwarewa da za ta taimaka wa gwamnatin kasar wajen shawo kan tsadar rayuwa da kuma wasu matsaloli kamar yadda BBC ta kalato.
Ya ce gwamnati za ta yi aiki da shawarwarin da kwamitin ya bayar wajen ganin ta yi amfani da albarkatun kasa yanda ya kamata.