Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda zai iya tuhumar Allah dangane da ƙaddara.
Sabon sarkin ya faɗi hakan ne yayin huɗubar sallar Juma’a a masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano.
Huɗubar dai ta mayar da hankali ne kan imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau.”
Duk wanda ya yi imani da Allah shi kaɗai to dole ne ya yi imanin duk abin da Allah ya ƙaddara.
Ba a tambayar ubangiji dalilin aiwatar da al’amura.An faɗa mana cewa duk wanda bai yarda da ƙaddara ba cewa daga Allah take, imaninsa bai cika ba.
Ya kamata mu zama masu godiya ga Allah a yanayi daɗi ko wuya.
Dole ne mu yarda cewa duk abin da ya faru a gare mu ta ƙaddara ce daga Allah, sannan abin da ba mu iya samu ba shi ma daga Allah ne.” In ji Sarki Sanusi.
Daga ƙarshe sarkin ya ja hankalin masallatan da su mayar da hankali kan kwana 10 na watan Dhulhijja da ke ƙaratowa.
“Watan babbar sallah na ƙara tunkarowa wanda kuma yana da matuƙar muhimmanci, ya kamata mu mayar da hankali wajen addu’o’i a kwanakin.” In ji Sarki Sanusi.