Qungiyar ASUU ta amince ta janye yajin aikin da ta dauki kusan wata takwas tana yi.
Duk da cewa ba a riga an sanar ba a qungiyance, wani jigo a qungiyar ya sanar da Jaridar Punch cewa sun amince a daren jiya cewa a janye yajin aikin.
Ya ce Shugaban Kungiyad ne zai sanar da hakan a safiyar yau, Juma’a.