Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya, ta yanke wa wani mai garkuwa da mutane Hamisu Bala da aka fi sani da Wadume da wasu mutane biyu hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.
Mai shari’a Binta Nyako ta samu Wadume da laifuka biyu daga cikin tuhume-tuhume 13 da ake masa tare da wasu biyu.
Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru uku a gidan kaso ga wani sifeton ‘yan sanda mai suna Aliyu Dadje, wanda shi ne jami’in ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Ibi a jihar Taraba, bisa laifin yin cuwa-cuwa da laifin boye mai laifi.
Bayan Wadume da Dadje, sauran wadanda ake tuhumarsu sun hada da Auwalu Bala wanda aka fi sani da Omo Reza, Uba Bala da aka fi sani da Uba Delu, sai Bashir Waziri wanda aka fi sani da Baba Runs, da Zubairu Abdullahi wanda ake kira Basho sai kuma Rayyanu Abdul.
Alkalin ya kuma yanke wa Delu, Abdullahi, da Abdul hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, yayin da ta sallami da kuma wanke Omo Razor da Baba Runs, akan daya daga cikin shaidun da suka gabatar.
Mai shari’a Nyako ta yanke hukuncin ne tun ranar 22 ga watan Yulin 2022.
An gurfanar da Wadume da sauran mutanen. da ake tuhuma a gaban kotu bisa tuhumar su da laifin satar mutane, kisa, ta’addanci da kuma sayen muggan makamai.
Laifin ya biyo bayan kashe wasu jami’an ‘yan sanda uku da wasu farar hula biyu a ranar 6 ga watan Agustan 2019 da wasu sojoji suka yi.
‘Yan sandan da ke cikin tawagar ‘sashen bibiyar bayanan sirri’ da ke Abuja, sun cafke Wadume ne a Ibi kafin sojoji su yi musu kwanton bauna a kan hanya.