BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An sake daga lokacin dawo da jirgin Kaduna-Abuja

Gwamnatin tarayya ta ce zirga-zirgar jiragen kasa na hanyar Abuja da Kaduna za ta dawo nan da kwanaki bakwai, da ga ranar 27 ga watan Nuwamba, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito daga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya.

Ministan Sufuri, Mua’zu Sambo ne ya bayyana hakan a yau Lahadin, yayin da ya ke duba gwajin jirgin da aka yi a kan titin jirgin kasan.

Ministan ya ce an yi hakan ne domin baiwa fasinjoji damar yin amfani da sabbin sharuɗɗa don jin dadin aikin jirgin.

Ya ce: “Batun ko jigilar jirgin za ta fara gobe ko ba gobe ba, ba mu ce za a fara aikin jirgin ba gobe.

“Ina so in yi bayani ƙarara game da hakan. Yanzu, mun bullo da wani sabon tsari kafin ka sayi tikiti.

“Sayan tikitin ku yana buƙatar samar da lambar waya da lambar shaidar ɗan ƙasa don yin ajiye bayanin fasinja, sabo da wannan shine farkon binciken tsaro.

“Don haka, a duk lokacin da jirgin kasa ya tashi daga wannan tasha zuwa waccan, mun san su waye da kuma wadanda ke cikin jirgin.

“Idan ba ku da NIN ba za ku hau jirgin mu ba. Wannan shi ne gaskiyar lamari,” in ji Ministan.

Leave a Reply