An kama wata ’yar sanda mai mukamin Mataimakiyar Sufeta da wata mai taimaka mata bisa zargin sato kananan yara biyar daga Jihar Sakkwato zuwa Abuja.
Daga cikin yaran da aka kama ’yar sandar mai suna ASP Kulu ta sato har da jaririya ’yar ƙasa da makonni biyu da haihuwa da wasu uku ’yan kasa da shekaru biyu.
Cikin ta biyar din sai wata ’yar shekara biyar ce, wadda aka sato ta a lokacin da take kan hanyarta ta tafiya makarantar Islamiyya a Sakkwato.
Rundunar ’yan sandan Abuja ce ta kama ASP Kulu da mai taimaka mata ne, a lokacin da suke dawowa daga Sakkwato a cikin bas din haya mai dauke da mutane 18.
Ana tsakar tafiya ne dai sauran fasinjojin suka lura cewa babu wadda ta shayar da jinjirar, wadda bisa dukkan alamu yunwa take ji.
Wani fasinjan motar mai suna Abba Danbaba da kuma Kwamared Nura Mukhtar na kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Network a Najeriya sun shaida wa wakilinmu cewa:“A ranar Asabar 27 ga watan Afrilu muna cikin tafiya sai muka lura yaran ba sa cikin hayyacinsu kuma ba sa magana.
“Don haka, yayin da muka sauka a Deidei, sai muka tambaye su don tabbatar da ko ’ya’yansu ne, sai suka ce eh, ’ya’yansu ne.“
Ita ’yar sandar da ke rike da jaririyar ta shaida mana cewa ba ta iya shayar da ita ne saboda tana fama da ciwon nono.
“Da jin haka sai muka sanar da ’yan sanda kuma da zuwa suka kai wadanda ake zargin ofishinsu da ke Gwagwa.
RFI Hausa