Rundura ƴan sanda a jihar Kano sun sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano.
A wani sako da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano.
Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu’ammali da ƙwayoyi masu sa maye kamar yadda muka ruwaito daga BBC.
A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.
A jiya ne dai aka ruwaito cewa matashin ya caccaka wa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.