Tattaunawa

An kai Buhari kotu kan kin bincikar Ganduje

Wata kungiyar da ke fafutukar ganin an yaki cin hanci da rashawa da kuma kokarin tabbatar da adalci SERAP, ta shigar da karar Shugaba Muhammadu Buhari, kan abun da ta kira “kasa bai wa ministan shari’a umarnin bincikar badakalar cin hanci da ake zargin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da shi.

Kungiyar ta shigar da karar ne a wata babbar kotu da ke Ikoyi a jihar Legas.

A watan Nuwamba ne dai kungiyar SERAP ta umarci shugaban kasar da ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan Gwamna Ganduje, tana mai cewa “domin gurfanar da shi a gaban kotu a karshen wa’adinsa idan an samu kwararan hujjoji.”

Haka kuma kungiyar ta bukaci a bai wa dan Ja’afar Ja’afar kariya, wato dan jaridar da ya wallafa bidiyon da ke nuna gwamnan yana karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila a jihar

SERAP ta ce har yanzu Shugaba Buhari bai ce komai ba tun bayan da ta gabatar masa da wasikar neman ya yi wannan abu.

A makon da ya gabata, wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da majalisar jihar daga ci gaba da binciken da ta fara na zargin karbar cin hancin dala miliyan biyar din da ake yi wa Gwamna Ganduje.

daga BBC

Leave a Reply