Sufeto-Janar na ƴansanda, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin dakatar da amfani POS da sauran na’urorin hada-hadar kudi ta wayar salula a cikin ofisoshin ƴansanda da sauran cibiyoyin ƴansanda a fadin kasar nan.
Egbetokun ya ce haramcin ya zama wajibi ne biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka yi kan yadda ma’aikatan ƴansanda ke yin hada-hadar kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya ta amfani da POS.
Shugaban na ƴansandan, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce haramcin na da nufin kiyaye mutuncin aikin ƴansanda da kuma tsaron ayyukan su.
Ya kuma jaddada cewa, an bada umarnin ne don dakile ayyukan cin hanci da rashawa da ake gani.
Babban Sufeto-Janar din ya ce duk wani jami’in da aka kama ya karya dokar to zai dandana kudar sa.