Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kai hari a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shinkafi inda mazauna yankin suka ce ”an kashe a kalla mutum 42.”
Maharan dai sun kai harin ne a kauyukan da suka hada da Kurya da Kursasa da wasu kauyuka da ke yankin inda suka yi ta harbin mai uwa da wabi.
A hirar da BBC ta yi da Dakta Suleiman Shuaibu Shinkafi wanda shine Sarkin Shanun Shinkafi, ya bayyana cewa wannan ba sabon abu ba ne irin wannan harin da ake kai masu a wannan yanki.
Ya bayyana cewa ”kimanin mutum 42 ne aka kashe a harin.”
Sai dai mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Malam Ibrahim Dosara, ya shaid wa BBC cewa mutane 28 ne suka rasa rayukansu a hare-haren a kauyuka biyar.
Amma wasu kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa sun tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu inda ya tabbatar da cewa mutum 10 ne aka kashe a kauyen Kursasa.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da rashin tsaro inda jama’ar jihar ke kokawa dangane da yawaitar garkuwa da mutane da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Abdullaziz Yari ya bayyana cewa maharan da ke kai hari na amfani ne da bindigogi “na al’ada” wato kanannan bindigogi inda kuma jami’an tsaro na amfani da manyan bindigogi inda ya bukaci jami’an tasron da su fito su yi amfani da manyan bindigoginsu domin yakar maharan.
Ya kuma bayyana cewa sai gwamnatocin jihohin da ke makwabtaka da jiharsa sun hada gwiwa, kafin a samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar yankin.