Uncategorized

An gida sabon asibitin Coronavirus cikin kwana biyar a China

China ta kammala gina wani babban asibiti cikin kwana biyar domin kula da masu dauke da kwayar cutar coronavirus.

Ranar Litinin ne kasar za ta bude asibitin Huoshenshan mai fadin murabba’in mita 14,000 da ta gina bayan bullar bakuwar cutar.

Hukumomin China sun ce asibitin Huoshenshan zai dauki gado 1,000, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta ayyana coronavirus a matsayin babbar annoba a duniya. Mutum 14,000 sun kamu da ita kuma ta kashe mutum 304, inji gwamantin China. Ana zargin wasu mutun 100 a kasa 22 na dauke da kwayar cutar.

A ranar 24 ga watan Janairu ne China da tura manyan motoci da kayan aiki domin aikin gina asibitin.

Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a duniya ya haura na annobar cutar Sars wadda kasa da mutum 30 suka kamu da ita a shekarar 2003. Mutum 8,000 ne suka kamu da kwayar cutar Sars a tsawon lokacin.

Leave a Reply