BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ambaliya ta shafi mutane sama da rabin miliyan a Najeriya

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya, NEMA, ta ce sama da mutum dubu ɗari biyar ne ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar.

Shugaban Hukumar ta NEMA a Najeriya Dr Mustapha Habib Ahmad ne ya shaida wa BBC hakan a Kano, inda ya ce suna fargabar cewar za a kuma samu ƙaruwar adadin, kasancewar akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a ƙarin wasu jihohin sakamakon ruwan da aka sako daga madatsar ruwa ta Lardu da ke jamhuriyar Kamaru.

Dr Mustapha ya ce yawan ruwa da ake da shi ya sa dukkan jihohi da ƙauyukan da ke kusa da kogin Neja da na Benue na cikin haɗari. Ya ce hasashen da hukuma ta fitar game da ambaliyar ruwa a bana, an ga jihohi 32 da ambaliyar ruwan za ta shafa kuma “mun tura wa duka ƙananan hukumomi”.

“Mun bai wa jihohi shawara da su kafa kwamitin gaggawa saboda aikin dole daga ƙasa za a fara ba daga sama ba – da an yi tsari mai kyau, da an kaucewa ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi, a cewarsa kamar yadda BBC ta ruwaito.

A cewarsa, batun sauyin yanayi yana taka rawa wajen sauye-sauyen da ake samu game da saukar ruwan sama. Ya bayyana cewa a bana, ruwa ya ci gaba da sauka har watan da muke ciki na Satumba saɓanin yadda aka gani bara da ruwan sama ya ja baya da wuri.

 

Leave a Reply