Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya ja hankalin ‘yan kasar kan muhimmancin kare ‘yancinsu da kuri’arsu a babban zaben 2023.
Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake shirin gudanar da taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan takara na jam’iyyun siyasa gabannin yakin neman zabe.
Taron zai kuma kunshi sauran masu ruwa da tsaki inda za a sanya hannu a rukuni biyu.
Na gabanin fara yakin neman zabe da kuma gab da babban zaben kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa, kamar yadda muka kalato daga BBC.
can baya dai an saba kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin ‘yan takara kafin zabe.
Sai dai a wannan lokaci an ga sauyi, saboda tabbatar da cewa komai ya tafi a cikin lumana.
Janar Abdulsalami da ke jagorantar kwamitin kokarin ganin an wanzar da zaben Najeriya cikin lumana ya ce sun lura da cewa a zabukan baya, mutane saboda talauci sun rinka sayar da yancinsu.
Ya bayar da misali da zaben 2019 inda ya ce mutane har ganye suke rikewa da ke nuna alamar za su sayar da kuri’arsu saboda hali na tsananin matsi.
A cewar tsohon shugaban wannan na daga cikin dalilan da suka sa a wannan karon suka lashi takobin fadakar da ‘yan kasar kan sanin mutuncinsu.
Tare da tabbatar da cewa sun yi zaɓe na-gari cikin cancanta, na mutumin da ya dace.