A makwanni biyu da suka gabata, mun kawo muku takaitattun bayanai game da amfanin wasu daga cikin kayan marmari wanda muka ce da zarar an ambace su, ba a bukatar dogon sharhi a kai saboda yadda aka saba da amfani da su. A wannan makon za mu ci gaba da kawo muku bayanan a takaice na kayan amfanin gona da aka fi nomawa a lambu wanda likitoci suke jaddada muhimmancin amfani da su a cikin kayan abincinmu na yau da kullum. Kamar yadda Likitoci suka yi bayani, an so a yi amfani da kayan marmari kafin a ci abinci, amma idan ba a samu dama ba zai fi kyau a yi amfani da su bayan kamar minti 30 da cin abincin. Wannan ya fi amfanar da jiki da sanadaran da ake bukata. Ga ci gaban bayanan muhimmancin wasu daga cikin kayan amfanin gonan wurin gina jiki da inganta lafiya:
Ayaba
1. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya.
2. Yana kara karfin kashi.
3. Ayaba na kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini sannan kuma yana samar da sauki wa mutanen dake fama da cutar.
4. Yana hana bacewan ciki(zawo).
Wake
1. Yana taimakawa wajen wanke ciki musamman yara kanana.
2. Yana rage taruwan kitse a jiki.
3. Samar da kariya akan cutar siga sannan kuma yana samar da sauki wa mutanen dake fama da cutar siga.
4. Kawar da cutar daji.
Kabeji
1. Yana wanke ciki musamman yara kanana da suke yawan fama da hakan.
2. Kare mutum daga kamauwa da cutar zuciya.
3. Kawar da cutar daji.
4. Yana kuma rage kiba a jiki.
Karas
1. karas na kara karfin ido.
2. Kare zuciyar mutum daga cututtukan dake kama zuciya.
3. Yana kawar da cutar daji.
4. Rage kiba a jiki.
Tafarnuwa
1. Kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini.
2. Kawar da cutar daji.
3. Rage kiba a jiki.
Inabi
1. Kare zuciyar mutum daga cututtukan dake kama zuciya.
2. Hana shanyewar shashen jikin mutum.
3. Kare maza daga kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraine.
4. Taimakawa wajen motsa jini
5. Kara karfin ido.
Shayin da ake kira da ‘Green Tea’ da turanci
1. Kawar da cutar daji.
2. Yana hana mutum kamuwa da cutar zuciya.
3. Kawar da cutar dajin dake kama ‘ya’yan golayen na maza.
4. Yana rage kiba a jiki.
Zuma
1. Zuma na warkar da rauni, konar wuta a jiki.
2. Yana warkar da mura.
3. Yana taimakawa wajen yin numfashi yadda ya kamata
4. Yana maganin cutar asma.
5. Kawar da cutar gyambon ciki.
6. Kawar da cutar daji.
7. Yana taimakawa wajen narkar da abinci a ciki.
8. Zuma na kara karfin kashi.
Lemun team
1. Kare mutum daga cutar zuciya.
2. Kawar da cutar daji.
3. Yana gyara fatar jiki.
4. Samar da sauki wa masu fama da cutar hawan jini kuma da kariya da ga kamuwa da cutar.
5. Yana maganin hucewar mura.
Man zaitun
1. Kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
2. Gyara fatar jiki.
3. Kawar da cutar siga.
4. Yana rage kiba.
Albasa
1. Yana kawar da cutar sanyi.
2. Kare mutum daga cutar zuciya.
3. Yana rage kitse.
Lemun zaki
1. Yana kara karfin garkuwa a jiki.
2. Maganin mura da hucewar mura.
3. Taimakawa wajen yin numfashi yadda ya kamata.
Abarba
1. Yana warkar da mura.
2. Kara karfin kashi.
3. Hana ami da gudawa.
4. Taimakawa wajen narkar da abinci a cikin mutum da sauri.
Tumatir
1. Kawar da cutar daji musamman wanda ke kama ‘ya’yan golaye.
2. Rage kiba a jiki.
3. Yana warkar da rauni a jikin mutum.
4. Kara karfin kashi.
P. Abada ko kuma Asala (Walnut)
1. Kare zuciyar mutum daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
2. Kawar da cutar daji.
3. Bunkasa kwakwalwa.
Kankana
1. Yana hana karancin ruwa a jiki.
2. Rage kiba.
3. Kare maza daga gcutar dajin dake kama ‘ya’yan golaye.
4. Kare mutum daga cutar shanyewa sashen jiki.
5. Kawar da cutar hawan jini.
Tufa (Apple)
1. Yana rage cutar zuciya.
2. Yana wanke cikin mutum musamman kananan yara.
3. Karfafa karfin gabobi.
4. Kawar da cutar dajin dake kama dubura da ‘ya’yan golaye.
S. Fiya (Abocado)
1. Kawar da cutar siga (Diabetes)
2. Kare mutum daga kamuwa da cutar shanyewar sashen jiki.
3. Kawar da cutar zuciya.
4. Gyara fatar jiki.