Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da fashewar bam a jiya Lahadi da daddare a unguwar Kabala ta da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Kakakin rundunar, Mohammed Jalinge ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, kamar yadda Daily Nigerian ta kalato daga NAN.
Ya ce ana da tabbacin fashewar bam ce da ta faru da misalin ƙarfe 9:45, inda ya ƙara da cewa fashewar ba ta samu kowa ba sabo da babu kowa a cikin ginin da abun ya fashe.
Ya ƙara da cewa tuni jami’an cire bam su ka isa gurin domin yin nazari.Jalinge ya yi alkawarin cewa zai sanar da sakamakon nazari da binciken da a ka yi da zarar an kammala.
Jim kadan bayan samun labarin ne, sai Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa tana gargadin mutanen jihar da su kasance cikin lura domin akwai rahoton sirri da ke nuna ‘yan ta’adda suna shirin tayar da zaune tsaye ta hanyar sanya bama-bamai a wajen tarukan mutane a fadin jihar.