Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood Zainab Indomie ta ce kwanaki hudu a daura aurenta da masoyinta aka fasa daura auren.
Indomie ta bayyana haka cikin wata hira ta musamman da ake da jarumai maza da mata a Gabon show room da jaruma Hadiza Gabon ke jagoranci.
Sai dai Indomie ta ce “fasa yin aurenta a kwanaki hudu kafin daura shi gangancina ba zai sa hakan ba Allah ne kawai bai kaddara hakan ba” in ji ta kamar yadda wata jaridar Qungiya Hausa ta ruwaito daga Gabon’s Room Talk Show.