Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, ya musanta garkuwa da kuma kashe ta.
A yau Litinin ne a ka sake kawo Tanko, da abokan aikata laifin da a ke zargi, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin Alƙali Usman Na-Abba.
Bayan da a ka karanto musu tuhume -tuhumen da a ke yi musu, dukkan su sun musanta.
Da a ke tuhumar Tanko cewa ya yi garkuwa da kuma kashe Hanifa, sai ya ce “ban aikata ba.”