Zababben Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bada shawara a dakatar da duk wasu gine-gine da ake yi a makarantu da asibito da kasuwanni.
Ana dai zargin gwamnatin Kano mai ci ne da cefanar da wasu filayen makarantun da asbitocin ga ‘yan kasuwa.
A cewarsa, “Kamar yadda muka kuduri aniyar dawo da tsarin birnin Kano; Ina shawartar Jama’a da su daina duk wani aikin gine-gine na filayen gwamnati a ciki da wajen makarantu, wuraren addini da na al’adu, da dukkan asibitoci, da makabarta, da kuma gefen katangar birnin jihar Kano,” inji shi.