Yan Kannywood sun karyata maganar Ladin Cima cewa ba ta taba samun kudi sama da dubu 20 ba.
Nazir Adam Salihi Wanda shi ne maubucin Gidan Badamasi ya ce, ‘na biya Ladi Cima (tambaya) dubu arba’in a fim din Gidan Badamasi Kashi na uku; na sake biyan ta dubu talatin a Kashi na hudu, Haka nan ko wata daya ba a yi ba na sake biyan ta naira dubu talatin a wani dan bidiyo na fadakarwa Kuma a duka ba ta yi fitowa sama da goma ba. Haka nan mun yi gyaran scene guda Wanda magana kawai ta yi muka biya ta dubu biyar muka Kuma sai mata abinci na dubu kusan hudu a wuni guda. Haka Nan a gabanta Hadiza Gabon ta ba ta dubu dari biyu da saba’in kyauta! Amma duk da Haka ka ji halin Dan Adam. Kai jama’a!!”
Shi ma Ali Nuhu ya ce a tambaye ta nawa ya biya ta a fim din Alaqa.