Wata kotun daukaka kara dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, karkashin mai shari’a, Jostis Peter Ige, ta jingine hukuncin da wata babbar kotun tarayya tayi akan tabbatar da Shehu Wada Sagagi a matsayin halattaccen shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano.
Kotun tace wannan rikici ne na cikin gida da ya shafi jam’iyyar, saboda haka uwar jam’iyya ta kasa na da damar rusa shugabancinta na jihar Kano.
A baya dai kwamitin kolin jam’iyyar PDP na kasa, ya sanar da rusa shugabancin Sagagi bisa zargin yana yiwa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso aiki, wanda kuma shi ne ya ayyana shi a shugabancin jam’iyyar na jiha a lokacin da yake cikin jam’iyyar, kafin daga bisani ya koma jam’iyyar NNPP harma ya samu tikitin takarar shugaban kasa, abinda jam’iyyar PDP ke ganin anyi mata kitso da kwarkwata kamar yadda Nasara Radio ta ruwaito.